SABUWAR HANYAR DA 'YAN DAMFARA KE SATAR BA TARE DA KA CIKE FORM DINSU BA.
Assalamu Alaikum jama'a barkanmu da wannan lokaci sannunku da sake kasancewa damu a wannan shafi namu mai Albarka.
A yau nazo muku da wani bayani akan sabuwar hanyar da yan damfara suke amfani da ita wajen satar muku kudi kokuma a wani abun a waya ba tare da kun danna Link ko cika wani form na su ba.
BA DOLE SAIKA CIKE WANI TSARI KO FORM AKE SATAR MAKA KUDI BA.....
Akwai wani tsari da yan damfara suka fito dashi a kwanannan, kamar yanda muka sani akwai wani VIRUS da hakas suke amfani dashi mai suna (trojan virus) wanda yake bawa mai shi damar sarrafa waya ko computer ka batareda saninka ba, saidai shi wannan trojan din dole saida yardarka kafin ya zauna acikin wayarka ko computerka shiyasa wasu lokutan hakas sunfi amfani da ababen yau da kullum kafin su sami damar yi maka kutse, misali awasu lokutan awayrka zaka rika ganin vidoes ko photo na batsa wanda kai bakasan ya akayi ka gansu ba asaman wall din wayarka tou idan kace zakakalla kana danna link din shikenan ka baiwa (trojan virus) damar zama cikin wayarka, wasu kuma tallan littafi wasu agogo, kowa dai da yanda suke bibiyar wayarshi suga me yafi so.
To yanzu sun daina amfani da trojan virus wani sabone zaa turo maka sako da unknown number kamar yadda kuka gani a message dina, da zaran ka bude sakon kuma har ka danna download shikenan ka baiwa virus din damar zama a wayarka, kuma zasuna amfani da wayarka su kwashe maka sirrin bankinka da kudadenka, haka kuma su hakass da scammers kullun cikin bincike da salon hanyar zaluntar al'umma suke bai zama wannan ce kadai hanyarda suke amfani da ita ba, dan haka sai mun kiyaye, kubar shiga kowanne link da sunan wai wani dan takara zai bada kuddi, indai ba kun aminta da link din bane.
Allah ya karemu baki daya🙏
Please kuyi share domin wasu su amfana
0 Comments